29 Yuni 2020 - 06:59
Turkiya Tana Shirin Fara Hako Man Fetur Da Iskar Gas A kasar Libya

Ministan makamashi na kasar Turkiya Fatih Do Namaz ne ya bayyana haka a jiya Lahadi, yana mai cewa; kasarsa tana shirin yin aiki tare da ma’aikatar man fetur ta kasar Libya...

(ABNA24.com)  Ministan makamashi na kasar Turkiya Fatih Do Namaz ne ya bayyana haka a jiya Lahadi, yana mai cewa; kasarsa tana shirin yin aiki tare da ma’aikatar man fetur ta kasar Libya dangane da hako man fetur da gas a kasar, sannan kuma ya yi ishara da cewa za su yi aiki akan batun tare da wasu kamfanonin kasa da kasa.

Do Namaz wanda wata tashar talabijin din kasar ta Turkiya ta yi hira da shi, ya kara da cewa; Wajibi ne a yi amfani da albarkatun man fetur din da kasar Libya take da shi domin gina wannan kasar da kuma samarwa da ‘yan kasar abubuwan more rayuwa.

Har ila yau, ministan makamashin na Turkiya ya yi ishara da yadda kasarsa take kashe dalar Amurka da ta kai biliyan 40 a kowace shekara domin shigar da makamashi,amma ya zama wajibi a rage yawan kudin ta hanyar samar da makamashi a cikin gida. Haka nan kuma ya yi ishara da cewa a shekarar da ta gabata, kasar ta samar da kaso 62% na makamashi ne ta hanyoyin cikin gida.


/129